
Uwar jam’iyyar APC ta kasa reshen jihar Enugu, a ranar lahadi ta bayyana goyon bayan ta na Shugaba Buhari ya zarce a Shugabancin najeriya a shekarar 2019.
Bayan haka kuma, jam’iyyar ta sake jaddada mubayi’atta ga Shugabancin Ben Nwoye a matsayin Shugaban jam’iyyar ta APC a jihar.
Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne a yayin wani zama na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar, wanda ya gudana a harabar Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa.
A lokacin da yake shaidawa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, Shugaban jam’iyyar Ben Nwoye, ya bayyana cewar jam’iyyar zata samar da dukkan ‘yan takarkaru a kowanne mataki na zabe.
A cewar Msta Nwoye, Gidan Zaki, wanda shi ne fadar Gwamnatin jihar ta Enugu, shi ne muradinsu a zaben da ke tafe, kuma suna yin duk abinda ya dace domin cimma wancan buri da muradi nasu.
“Muna da dukkan dama, da kuma zarafin fuskantar jam’iyyar PDP mai mulki domin kwacee goruba a hannun kuturu a 2019” A cewar Shugaban.