
Reshen jihar Lagas na jma’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun sanya kafa sun yi fatali da batun karawa Shugaban jam’iyyar na kasa John Oyegun lokacin, domin cigaba da kasancewarsa Shugaban jam’iyyar, sun bayyana cewar wannan karin lokaci ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan sun tattauna da dukkan bangarorin jam’iyyar na masu ruwa da tsaki wanda suka halarta a ofishin jam’iyyardake Marina a Legas din, a cewar uwar jam’iyyar reshen jihar Legas.
A lokacin karkare zaman tattaunawar, Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewar, karawa Shugaban jam’iyyar na kasa lokaci, wannan abu ne da ya sabawa tanade tanade na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Mista Oyegun dai na zaman doya da manja ne a yanzu haka tsakanin da jagoran jam’iyyar na kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne ke juya jam’iyyar reshen jihar Legas.
“Sashi na 223 a cikin kundin tsarin mulkin 1999, yayi bayanin hanyoyin da ya kamata abi idan wa’adin Shugaba ya kare a matakin shugabancin jam’iyya”
A cewar uwar jam’iyyar wannan sashi na 223 a kundin tsarin mulkin Najeriya yayi bayanin hanyoyin da ya kamata abi idan lokacin mai rike da mukamin Shugaban jam’iyya ya kare, ba irin yadda aka yi ba.
Haka kuma, sashi na 17 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya nuna cewar Shugaban jam’iyyar zai yi wa’adin mulki na shekaru hudu ne kawai, wanda kuma ana iya sake sahale masa wasu shekaru hudun masu zuwa. sabanin abinda aka yi.
A lokacin da yae zantawa da manema labarai, abayan kammala zaman taron, Shugaban jam’iyyar reshen jihar Legas ta tsakiya, Tajudeen Olusi, yace yanke hukuncin da majalisar zartarwar jam’iyyar ta kasa ta yi na karawa Mista Oyegun shekara daya ya saba da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.