Home Labarai Jam’iyyar APC ta amince Oyegun ya cigaba da jan ragamar ta na shekara daya

Jam’iyyar APC ta amince Oyegun ya cigaba da jan ragamar ta na shekara daya

0
Jam’iyyar APC ta amince Oyegun ya cigaba da jan ragamar ta na shekara daya
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, John Oyegun

Shugaban jam’iyyar APC na kasa,  ya samu karin wa’adin cigaba da Shugabancin jam’iyyar na tsawon shekara guda.

An cimma yarjejeniyar amincewa da karawa Oyegun cigaba da kasancewa Shugaban jam’iyyar a wani taron masu ruwa da tsaki jam’iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta.

taron dai shi ne irinsa karo na farko a wannan shekarar da jam’iyyar ta yi tare da kwamitin amintattun jam’iyyar suka yi, wanda Ministoci da Gwamnoni da jiga jigan jam’iyyar APC daga jihohi 36 da suka halarci zaman.

Haka kuma, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki bai halarci wannan zaman taron ba, wanda kakakin majalisar dokoki Yakubu Dogara ya halarta tare da mambobin majalisar dokoki ta tarayya.

Daga cikin wadan da suka halarci wannan taron har da Gwamnan Benuwai Samuel Ortom wanda a baya ya nuna ba zai halarci taron ba, sabida batun rikicin manoma da makiyaya.