
Reshen jam’iyyar PDP na jihar Legas a daren lahadi ya ayyana goyan bayansa ga takarar Cif Olabode George a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa baki daya a zaben sabbin Shugabannin jam’iyyar na kasa da za’a yi ranar 9 ga wannan watan, a wajen babban taron jam’iyyar na kasa da za ayi.
Mashood Salvador, shi ne shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar ta Legas, shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da aka yi tsakanin Bode George da Shugabannin jam’iyyar reshen jihar Legas a sakatariyar jam’iyyar dake unguwar turawa ta Ikeja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya ruwaito cewar, Bode George ya shagaltu da yakin neman zabe a yankin kudu maso yamma na Yarabawa zalla gabanin zaben Shugabancin jam’iyyar da za a yi nan gaba kadan.
Ya zuwa yanzu dai, kimanin mutum takwas ne suka fito takarar neman Shugabancin jam’iyyar daga yankin kudancin kasarnan, mutanan dai sun hada da; Tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel da kuma tsohon ministan ilimi Tunde Adeniran.
Sauran sun hada da, tsohon ministan matsa Taoheed Adedoja da kuma tsohon dan takarar Gwamnan jihar Legas a zaben da ya gabata na 2015, Jimi Agbaje da Yarima Uche Secondus wanda ya taba rike mukamin shugaban riko na jam’iyyar, da kuma cif Remond Dokpesi shugaban kamfanin Daar, me mallakar gidan talabijin na AIT.
Mista Mashood Salvador, ya ce “A madadin reshen jihar Lagas na jam’iyyar PDP, muna tabbatar da dukkan goyon bayanmu ga cif Bode George a zaben da za a yi ranar tara ga wannan watan na Disamba, a sabida haka, yankin kudu maso yamma, shi ne yafi cancantar rike shugabancin PDP”
A tsohon shugabancin jam’iyyar dai, jihar Ekiti ita ta samar da mataimakin shugaban jam’iyyar mai wakiltar shiyyar kudu maso yamma, daga nan sai jihohin Oyo da Osun da suka dafe manyan mukaman jam’iyyar a mataki na kasa, jihar Legas ce kadai bata samu komai, dan haka yanzu burinmu shi ne, samar da Shugaban PDPna kasa.