
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta kafe cewa ba za ta janye yajin aikin da ta ke yi ba duk da rashin biyan su albashi tun watan Febrairu.
Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels Television, a shirin Sunrise Daily na yau Talata, wanda wakilinmu ya naɗa.
Yayin da ya ke zargin gwamnatin tarayya da amfani da “yunwa” a matsayin makami wajen tilasta wa malaman da ke yajin aikin komawa ajujuwansu, Mista Osodeke ya ce duk da haka kungiyar ba za ta bada kai bori ya hau ba.
“An riƙe mana albashin, wata na shida kenan ba a biya mu albashi ba. Sun dauka idan sun rike albashin mu wata biyu ko uku za mu ji matasi har mu zo mu roke su mu ce za mu koma bakin aiki.
“Amma mu a matsayinmu na ƙungiyar masu hankali da ilimi, mun girmi haka. Ba za ku iya amfani da karfin yunwa don sanya mu janye yajin aiki ba,” in ji shugaban ASUU.