Home Labarai Japan na fama da gidajen da babu mutane, sun yi kira ga baki su zo su zauna

Japan na fama da gidajen da babu mutane, sun yi kira ga baki su zo su zauna

0
Japan na fama da gidajen da babu mutane, sun yi kira ga baki su zo su zauna

Garin dadi na nesa, inji ‘Yan magana. A lokacin da al’umma da dama ke shiga cikin matsanancin halin wajen zama, amma a kasar Japan ba haka abin yake ba.

Kididdiga ta nuna cewar a shekarar 2013 akwai gidaje akalla miliyan 61 a kasar Japan yayin da al’ummar kasar suke miliyan 52 , indai bayanai suka nuna cewar gidajen kasar sun fi mutanan kasar yawa.

A saboda haka ne hukumomin kasar suka bukaci baki ‘yan kasashen waje da su je su nemi iznin zama a gidajen da babu Kowa.