
Gogaggen jarumin masana’antar fina-finai ta Nollywood, Lari Williams ya rasu ya na da shekaru 81.
Williams ya rasu ne a gidansa da ke Ikom a Jihar Cross River a jiya Lahadi, kamar yadda iyalinsa su ka sanar a wata sanarwa da su ka fitar a jiyan.
Kafin rasuwar sa, marigayin ya shafe kusan shekaru hamsin yana fim a Nollywood, inda ya yi finafinai kamar su Village Headmaster, Ripples, Mirror in The Sun da wasu saura da dama.
Williams marubucin waƙa ne kuma marubucin wasan kwaikwayo ne, in da ya samu lambobin girma da dama, har da ta OFR a 2008.
Shine shugaba na farko gamayyar jaruman finafinai ta Nijeriya.