
Fassarawa: Garba Shehu
Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari Da Ya Gabatar A Taron Majalisar Dinkin Duniya, Game Da Matsayin Nijeriya A Kan Muhimman Batutuwa Da Suka Shafi Duniya, Wanda Ya Gabatar A Ranar, 25 Ga Satumba, 2018.
A ranar Talatar da ta gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa duniya matsayin Nijeriya game da wasu muhimman batutuwa da suka shafi duniya a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 da ya gudana a birnin New York. Yayin jawabin nasa, da farko Shugaba Buhari ya soma ne da jinjina wa Tsohon Babban Sakataren Majalisar marigayi Kofi Annan, game da irin gudunmawar da ya bayar wajen wanzar da lumana a fadin duniya a halin rayuwarsa.
A cewar Shugaba Buhari, “Yayin da mu ‘yan Afirka ke jimamin rashin gwarzon dan mu wanda duniya ta san da shi, ta bi sawunsa wajen koyi da kyawawan ayyukansa don ci gaban al’umma.
Marigayin ya kwatanta halin da’a da son juna da kuma sadaukarwa don tabbatar da gaskiya da adalci da kuma kare hakkokin dan-Adam. Shugaba ne mai hangen nesa da zaburarwa, wanda ya shafe rayuwar aikin sa a Majalisar Dinkin Duniya domin cimma manufofinta. Hakika duniya ta yi dadi da irin gudunmawarsa, madalla da kyawawan ayyukansa”.
Haka nan, Shugaba Buhari ya ce lallai duniya ta samu kyawawan sakamako da kuma alamomi masu saka kaimi a sakamakon ban gishiri in ba maka manda da aka yi a tsakanin kasashen duniya wajen yaki da matsalolin da suka addabi zaman lafiya a fadin duniya. Tare da yaba kokarin shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa da kuma Koriya ta Kudu, wajen la’akari da manufarmu ta kawar da makaman kare-dangi a yankin Koriya.
Kazalika, Buhari ya yaba da irin zaman lafiyar da Shugaba Donald Trump da takwaransa Kim Jong-Un suka nuna ta hanyar samar da shirin da ke bukatar bangarorin biyu su ci gaba da mu’amala ta alheri a tsakani.
Sa’ilin da yake nuna damuwarsa game da wasu kalubalan da suka dabaibaye zaman lafiya da fanni tsaro a sassan duniya, Shugaba Buhari ya ce lamarin ya munana matuka a wasu wurare. Tare da bada misalin halin da Rohingyawa ke ciki a Myanmar, da batun Isra’ila da Falatsinawa, hada da yankunan Yemen da Siriya, da kuma irin fafatawar da ake yi da ‘yan ta’adda a gida da waje kamar Boko Haram da Al-Shabab.
A cewar Shugaba Buhari, “Matsalar ta’addanci da muke fuskanta, musamman ma a yankin Sahara da kuma tabkin Cadi, wasu matsalolin cikin gida ne ke ruruta matsalar, amma a yanzu abin ya karu ta yadda har da gudunmawar masu rajin jihadi daga kasashen ketare, hada da shigowar wasu ‘yan bindiga daga kasar Iraki da Syria, da kuma shigo da makamai daga Libya”.
Ta bakinsa, “An dan samu sassauci a Myanmar. Don haka ne ma muke yaba kokarin Majalisar Dinkin Duniya da iri tsayin dakan da ta yi a tsakanin Rohingyawa wajen ganin cewa rikicin yankin ya zo karshe, tare da hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu wajen haddasa fitina a yankin da ta yi sanadiyar salwantar rayuka da dimbin dukiyoyi.
Buhari ya yi kira ga kasashen duniya da su matse kaimi wajen magance matsalolin da kan faru sakamakon kabilanci da kuma addini. Daga nan shugaban ya jaddada cikakken goyon bayan Nijeriya ga majalisar wajen tabbatar da al’ummar Rohingya sun samu zarafin komawa matsugunnan su a Myanmar cikin tsaro da kuma kariya masu inganci da mutunci.
A bangare guda, Shugaba Buhari ya yaba da kokarin gwamnati da ma al’ummar kasar Bangladesh, hada da sauran kasashe da kungiyoyin da suka bada gudunmawar su wajen taimaka wa ‘yan gudun hijirar Rohingya. Yayin da kuma yake jan hankalin kasashen duniya dangane da irin wahalar da jama’ar Syria da Yemen ke ciki, a nan ma Buhari ya bayyana cewa lallai bai kamata a yi kasa a gwiwa ba wajen ceto al’ummar yankunan. Ya ce, “Dole ne mu yi dukkan mai yiwuwa wajen samar da lumana game da wadannan yake-yake wanda ba za a iya samun nasara a kansu ba da karfin bindiga kadai. Game da Syria kuwa, muna sa ran Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan shirin Geneva da na Sochi a karkashin jagorancin Rasha da Iran Turkiyya don cimma bukata.”
Ya kara da cewa, “Dole ne kasashen duniya su dage wajen karfafa wa bangarorin da lamarin ya shafa wajen yin amfani da matakin sulhu da makamantan sa wajen samun maslaha a tsakaninsu da kuma kawo karshen wahalar da yankunan Syria da Yemen ke fama da ita. Sannan mun yaba wa kasashen Turkiyya da Jordan da Girka da Jamus da Italiya hada da Faransa dangane da karbar milyoyin ‘yan gudun hijira da suka tafi neman mafaka a yankunan su”.
Game da rikicin yankin Gabas ta tsakiya da ke ci gaba da tsananta, Buhari ya yi kira ga al’ummar Isra’ila da Falasdinawa, da su dawo su waiwayi abin da zai haifar musu da zaman lumana da tsaro mai inganci ta hanyar la’akari da wasu dabarun da majalisar ta yi amfani da su a wasu wurare don cimma lumana da kuma dokin kasa da kasa. Kana ya nunar da cewa, rashin hada kai a gudanar da harka da kuma rashin daukar mataki mai muhimmanci kan taimaka wajen ruruta wutar rikici da kuma yin tarnaki ga zaman lumana da fannin tsaro a sassan duniya. Tare da danganta abin da ke faruwa a yankin Gaza ga yin amfani da karfin mulki ba a bisa yadda ya dace ba. Don haka ne Shugaba Buhari ya ce, Nijeriya na kira ga bangarorin biyu da su rungumi yin sulhu a tsakani domin cimma daidaito.
A bangaren abin da ya shafi kasar Habasha da Eritrea kuwa, da kuma kokarin da ake yin a wanzar da zaman lafiya a tsakanin Djibouti da Somaliya Buhari bai rasa ta cewa ba. Domin kuwa cewa ya yi, “Na yi ammanar cewa ta hanyar sadaukarwa da kuma aiki tukuru, maido da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya abu ne mai yiwuwa”.
A bangaren yawaitar ‘yan gudun hijira da akan samu wanda kan yi dalilin hasarar rayuka da makamantansu, Buhari ya aminta da matakin da aka dauka don dakile wannan matsalar wanda irinsa kenan na farko, inda ya yi fatan ganin an yi amfani da matakin Marrakech don samun daidaito. Tare da cewa dalilin wannan mataki kuwa shi ne, don kare hakkokin masu hijira fadin duniya.
Sa’ilin da yake yaba wa kasashen Jamus da Italiya da kuma Faransa dangane da kula da sha’anin masu kaura yadda ya kamata, Shugaba Buhari ya ce yawan kaura da akan samu barkatai ba rikici kadai ke haifar da hakan ba, har da sauyin yanayi da kuma rashin samun aikin yi a kasa, yayin da sauyin yanayi ya kasance babban kalubalen da zamanin mu ke fuskanta. “A kusa da mu muna ganin yadda makwabciyarmu Nijejar ke fama, da kuma raguwar tabkin Cadi duk a sakamakon sauyin yanayi”.
A baya tabkin Cadi shi ne babban hanyar samun biyan bukatun rayuwa ga mazauna yankin da yawansu ya kai sama da milyan. Shugaba Buhari ya ce sai dai a yanzu jama’ar yankin sun shiga halin talauci da matsin rayuwa sakamakon kafewar tabkin da kuma harkokin ‘yan ta’adda a yankin. Lamarin da a cewarsa ya shafi tattalin arzikin yankin, musamman ma a tsakanin manoma da makiyaya.
Domin shawo kan wannan wadannan matsaloli kuwa, Buhari ya ce abin da ake bukata shi ne ci gaba da neman hadin kan Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnatocin kasashen duniya hada da manya-manyan kungiyoyi da hukumomi irin su Hukumar Kula da Tabkin Cadi da Kungiyar Inganta Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma da sauransu.
Daga nan, Buhari ya jinjina wa Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Jamus da Norway da Sweden da Tarayyar Turai da Faransa da sauransu dangane da irin gudunmawar da suka bayar wajen kokarin magance matsalar da ke yankin Tabkin Cadi.
A kan abin da ya shafi rashawa da kuwa yadda ake hada-hadar kudade kuwa, Buhari ya ce wannan matsala ce babba da ke hana bunkasar zaman lafiya da kuma tattalin arzikin kasa a kasashe masu tasowa. Ya kara da cewa rashawa na hana gwamnatin kasa bai wa ‘yan kasa rayuwa mai inganci yadda ya kamata. Tare da cewa yaki da rashawa aiki ne da rataya a kan dukkan masu fada a ji. Tare da cewa, “Hakki ne a kanmu da ke bukatar a hada karfi da karfe wajen yaki da wannan matsala ta hanyar bincikawa da kuma hukunta wadanda ke da halin kwashe kudaden kasarsu zuwa wata kasa”.
A cewar Buhari, dukkan matsalolin da ake fuskanta a sassan duniya a yau, kama rashawa da fadace-fadace, ta’ammuli da makamai da sauransu, musamman ma a yankin Afirka, za a iya dakile su ne kawai idan aka dauki matakin zuwa a dunkule wuri guda don a yi aiki tare. Kuma hanya guda da za a iya bi don cimma wannan bukata ita ce ta hada kan kasashen duniya (misalin Majalisar Dinkin Duniya). “Wannan ne ma ya sa muke ci gaba da kira a kan a inganta hadin kan don samun karin karfin dukkan sassa yadda ya kamata”, inji Buhari.
Ta bakin Shugaba Buhari, “Ina mai tabbatar muku cewa a wannan jawabi nawa, nuni yake da yadda Nijeriya ya dauki wannan majalisar da manufofinta da muhimmanci. Daga lokacin da muka shige ta a shekarar 1960, mun bayar da gudunmawarmu yadda kamata a fannoni daban-daban kuma a wurare daban-daban. Tare da cewa a kowane lokaci Nijeriya a shirye take domin bada tata gudunmawa a inda ake da bukatar hakan domin samun daidaito
FASSARA: Garba Shehu
Babban Mai Taimakawa Na Musamman Ga Shugaban Kasa
Fannin Yada Labarai