Home Ƙasashen waje An jefe mace da na miji sakamakon yin zina a Afghanistan

An jefe mace da na miji sakamakon yin zina a Afghanistan

0
An jefe mace da na miji sakamakon yin zina a Afghanistan

 

An jefe wani mutum da wata mata bayan da a ka kama su sun yi zina a Arewa-maso-Gababshin Lardin Badakhshan da ke Afghanistan.
Wasu jami’an gwamnati ne guda biyu na Taliban su ka tabbatar da hakan a yau Laraba.
Wani jami’i ya shada cewa an jefe su biyun ne a kotun shari’ar Muslunci.
A Addinin Musulunci, haramcin ne mata da maza su yi saduwa da ba ta aure ba.
Hakazalika idan namiji mai aure ya yi zina da matar aure kuma a ka samu shaidu huɗu, to hukuncin su shine a jefe su har sai sun mutu.
Jami’in ya ce sun amsa laifin su kuma sun ce wajen sau biyu zuwa uku su na saduwa da juna.
Wata jarida ta ƙasar, Hasht-e Subh ta baiyana cewa an jefe su ne a ranar LitininLitinin a bainar jama’a a lardin Nasi.
An ce wani kwamandan Taliban ne ya babdaa umarnin jefe matar daga mutumin.