
Shugaban kngiyar jama’atu Izalatul Bid’a wa ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi juna wajen zaman lafiya da kuma yarda da juna, musamman tsakanin Musulmi da Kirista.
Shekh Bala Lau yayi wannan kiran ne, a taron da kungiyar ta JIBWIS ta gudanar a Jos babban birnin jihar Filato a karshen makon da ya gabata. Taron mai take “Wa’azin kasa na 2018a Jos”.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su bari kabilanci ko bambancin harshe ya raba tsakaninsu. Yace”Mun zo Jos ne domin yin wa’azi kan zaman lafiya da kuma kaunar juna a tsakanin ‘yan najeriya”
“Mu sani mu al’ummar wannan kasa ba mu da wata kasa da ta wuce wannan najeriyar, kada mu bari wasu su yi amfani da mu domin biyan bukatar kansu, dan mu sabawa juna ko mu yaki juna”
Sheikh Bala Lau, ya kuma yabawa Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong kan kokarinsa wajen dawo da zaman lafiya a jihar, sannan yayi kira ga Gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba da su yi koyi da takwaransu na Filato domin samar da zaman lafiya tsakanin al’ummarsu.