
Mansur Ahmed
Bayan Jigawa tayi Gwamnoninta na farar hula guda uku (3) an so jam’iyyar PDP ta cigaba da mulki a 2019 saboda tana da kundinta na tsari da aka rubuta yadda za’a tafiyar da ita tsawon shekaru 25, wadda a wannan tsarin shine za’a gama da maganar aikin hanya, lafiya, ruwan sha, makarantu, tarbiyyar mutane, kula da nakasassu, karatun ya’yansu, inganta tsaro, Samar da yanayin nutsuwa da fahimtar juna ga yan Jigawa, raya karkara da birane.
Kwatsam sai Allah ya jarrabi Jigawa da wani Gwamna mai suna Badaru Abubakar, ba shakka jihar Jigawa zuwa yanzu ta gamsu cewar tayi adon jamfa a saman babbar riga ga wadda bai gane Hausar ba ga abinda ake nufi (Mutum ne yayi wanka ya saka wando ya saka babbar riga sannan ya daukko karamar da ake sakawa a ciki ya saka a saman babbar rigar kuma ya fito sallar juma’a) a wannan gab’ar nasan mai karatu zai yi gajeren murmushi, bayan ya numfasa zai tambayi wai me Mansur yake nufi.
Tun a washe garin rantsar da Badaru a jawabinsa da jawabin shugaban jam’iyyar APC na Jigawa wadda yayi a filin rantsuwa a wani yanayi da murya irinta d’an asharalle, mahankalta da masu nazarin al’amuran siyasa a ciki da wajen k’asar nan suka bada tabbacin cewar Badaru ba zai iya yiwa Jigawa komai ba, dalili kuwa shine a lokacin da aka rantsar da Sule Lamido a matsayin Gwamna a 2007 tun daga filing rantsar dashi yan Jigawa suka fara gamsu cewar kwalliya za ta biya kudin sabulu, domin a jawabinsa bayan karbar rantsuwa yace gwamnatinsa a ta yi tafiya a tsari da yanayi iron na Malam Aminu Kano wajen mayar da talaka mutum.
Ya bayyana ilmin mata kyauta a kowanne mataki, ya bayyana daukar yara 100 domin fita dasu k’asashen waje karatu, ya bayyana alawus ga nakasassu da karatun ya’yansu maza da mata kyauta, ya bayyana shiri da tsarin haihuwa lafiya da fitowa da tsarin Gunduma health system, ya bada tabbacin Samar da zaman lafiya, tsaro, walwala tare da tafiya da kowanne fanni da rukunin al’umma, bai kammala jawabinsa ba sai da ya nemi bankunan da suke Jigawa da su bada gudunmawa domin a gyara makarantun kwana na jihar nan
Hon. Babandi Ibrahim Ibrahim wadda muke tare dashi a gidan gonarsa a ranar da ake rantsar da Badaru cewa yayi duk gwamnatin da kaga ta fara da zargi ko kushe wadda ta gabace ta to babu abinda za ta iya yi na arzik’i sai shirme, yave maimakon Badaru ya fad’i tsarin da yazo dashi kuma ya bayyana yin wasu a take amma ya fara da kushe mutumin da ko rabin aikinsa ba zai iya yi ba.
In kana so ka yarda da haka shine In ba lalacewa ba me zai kai gwamnan jiha biki bud’ewa injin bada kudi na banki (ATM), ko kaga gwamna yana kaddamar da rabon akuya a matsayin hangar arziki ko rabuwa da talauci, kaga Gwamna yana bada risho ko ana masa kyautar matashin kai (filo), ko kaga Gwamna yana sawa ana daukkowa motar hawa a gidan wadda ya gaje shi ai kasan abin babu dadi wai Hausawa su ka ce mahaukaci yaci kashi,
Badaru bai fita daga zuciyar talakan Jigawa ba sai a aka ga bashi da wajen zuwa ko a in yi bini-bini sai yace ya tafi China, Chinan nan ko bukka har yanzu ba mu ga yan Jigawa sun amfana da ita ba, kullum k’aryar Inji nan noma ake yiwa talakawa har yanzu da fartanya ake noma a Jihar.
Hoton da yake biye Gwamna Badaru ne yake gaisawa da mace, a addinin musulunci da al’adar Hausa/Fulani ban ga inda aka halasta haka ba amma wadda yake da hujja zai iya bani domin na gamsu, wadda bai gani ba kuma mu taru mu yiwa Badaru Addua Allah ya shire shi ya dena.