
Hassan Danbaba, jikan Sir Ahmadu Bello Saurdaunan Sokoto ya rasu.
Majiyoyi da ke kusa da iyalan Marigayin sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa Danbaba ya yanke jiki ya fadi, inda da ga nan rai ya yi halin sa a Kaduna a ranar yau Asabar.
Ya rasu ya na da shekara 51 a duniya.
Majiyoyin sun ce za a kai gasar tasa Sokoto a jirgin sama domin yi masa jana’iza.
Danbaba, wanda shi ne Magajin Garin Sokoto, shine shugaban rukunin otal na Stonehedge Hotels.
Ya rasu ya bar mata uku da ƴaƴa shida.
A watan Afrilun 2021 je mahaifiyarsa, Aishatu Ahmadu Bello, ta rasu tana da shekaru 75 a duniya.