Home Siyasa An jikkata mutane 74 yayin da a ke zargin ƴan daba sun kai hari kan tawogar Atiku a Maiduguri

An jikkata mutane 74 yayin da a ke zargin ƴan daba sun kai hari kan tawogar Atiku a Maiduguri

0
An jikkata mutane 74 yayin da a ke zargin ƴan daba sun kai hari kan tawogar Atiku a Maiduguri
Rahotanni da ga birnin Maiduguri na jihar Borno na cewa a kalla mutane 74 ne su ka jikkata, bayan wani hari da aka kai kan ayarin motocin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a Maiduguri, jihar Borno.
Abubakar dai ya na Maiduguri ne a ci gaba da yakin neman zabensa na 2023.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna motoci da dama da aka lalata sun nufi dandalin Ramat, wurin da aka gudanar da taron.
Da ya ke mayar da martani game da harin na Maiduguri, kakakin kwamitin yakin neman zaben PDP, Dino Melaye, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da daukar nauyin ƴan daba su kai musu hari.
Ya yi ikirarin cewa mutane 74 sun jikkata kuma suna karbar magani a asibiti.
“Sun so ne su hana mu gudanar da gangamin neman zaben mu, kamar yadda muke magana, mutane 74 sun jikkata kuma an kwantar da su a asibiti.
“‘Yan APC sun lalata motoci da dama,” in ji Mista Melaye.
Ba a samu nasarar jin ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Borno ba da s ka neme shi ta wayar tarho.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa a watan Oktoba ma an kai wani hari makamancin haka kan magoya bayan Abubakar a jihar Kaduna.