Home Kasuwanci Jirgin Air Nigeria zai fara tashi a 2022, in ji Hadi Sirika

Jirgin Air Nigeria zai fara tashi a 2022, in ji Hadi Sirika

0
Jirgin Air Nigeria zai fara tashi a 2022, in ji Hadi Sirika

 

Hadi Sirika, Ministan Harkokin Sufurin Jirgin Sama ya baiyana cewa jairgi mallakin Nijeriya, Air Nigeria, wanda a ka daɗe a na tsimaye, zai fara tashi a watan Afrilu na shekarar 2022.

Sirika ya baiyana hakan ne ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa a yau Laraba, jim kaɗan bayan an gama ganawar majalisar zartaswa ta mako-mako.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci ganawar a fadar shugabacin ƙasa a Abuja.

Ministan ya kuma baiyana cewa wani kamfani ne zai gudanar da harkokin Air Nigeria ɗin, in da gwamnatin tarayya kuma ta ke da kashi 5 na hannun jari.

Ya ƙara da cewa ƴan kasuwa a Nijeriya za su samu kashi 46, inda sauran kashi 49 kuka za a tanadarwa sauran masu son zuba hannun jari har da ma ƴan kasuwa da ga ƙasashen waje.

Ministan ya ƙara da cewa idan jirgin na ƙasa ya fara aiki, to zai samar da aikin yi 70,000 ga ƴan Nijeriya.

 

Daily Nigerian Hausa