Home Kasuwanci Jirgin Arik na roƙon fasinjoji da su dawo bayan ma’aikatan sa sun janye yajin aiki

Jirgin Arik na roƙon fasinjoji da su dawo bayan ma’aikatan sa sun janye yajin aiki

0
Jirgin Arik na roƙon fasinjoji da su dawo bayan ma’aikatan sa sun janye yajin aiki

 

Kamfanin jirgin sama na Arik Air ya sanar da cewa ma’aikatan sa sun janye yajin aiki kuma sun dawo bakin aiki.

Kakakin kamfanin, Adebanji Ola, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, ya ce tuni kamfanin ya ci gaba da jigilar fasinjoji har ma ya fi da.

A ranar Talata ne dai Kamfanin ya rufe bayan da matuƙa jiragen sa su ka tafi yajin aiki.

Kamfanin ya yi barazanar korar ma’aikatan bayan da ya ce yajin aikin nasu haramtacce ne sabo da basu sanar da kamfanin ba kamar yadda doka ta tanada.

“Muna baiwa fasinjojin mu haƙuri a bisa wannan abu da ya faru. Yanzu mu na sanar da cewa mun dawo aiki ka’in-da-na’in,” in ji Ola.