Home Ƙasashen waje Jirgin dakon kaya maƙare da makamai ya yi hatsari a hanyar zuwa Bangladesh

Jirgin dakon kaya maƙare da makamai ya yi hatsari a hanyar zuwa Bangladesh

0
Jirgin dakon kaya maƙare da makamai ya yi hatsari a hanyar zuwa Bangladesh

 

 

Wani jirgin dakon kaya ɗauke da mutum takwas a cikinsa ya yi hatsari a arewacin Girka wato kusa da birnin Kavala.

Kafar talbijin din kasar ta rawaito cewa jirgin dakon kayan mallakin wani kamfanin Ukraine ne, kuma ya tashi ne daga Serbia zuwa Jordan.

Haka kuma jami’a sun bayyana cewa jirgin yana ɗauke da tan 11 na makamai ciki har da nakiyoyi da za a kai Bangladesh.

Tun da farko sai da matukin jirgin ya nemi izinin saukar gaggawa a filin jirgin saman Kavala saboda matsalar injin da ya fuskanta, to amma daga baya sai aka daina jin duriyarsa.

Wasu hotunan bidiyo da ganau suka dauka sun nuna jirgin na ci da wuta kafin ya fadi kasa. Tuni jami’an kashe gobara suka isa wajen.