
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa aikin kafa kamfanin sufurin jiragen sama na ƙasa, Nigeria Air, ya kai matakin kashi 91 cikin 100 na kammala wa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a taron bibiya na ayyukan ministoci karo na 3 da aka yi a ranar Litinin a Abuja
A cewar Buhari wannan aikin zai tabbata ne tare da ba da takardar shaidar sahalewa ga filayen jiragen sama na Legas da Abuja daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa.
Ya ce filayen jirgin saman Kano da Fatakwal ana gudanar da irin wannan tsarin ba da takardar shaida.
Buhari ya kuma bada tabbacin cewa jirgin mallakin ƙasa da aka alkawarta zai fara aiki jirgin kafin ko kuma bayan watan Disambar wannan shekara.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa samar da Nigeria Air zai lakume Naira biliyan 14.6, a karkashin kashi biyar bisa dari na hannun jarin gwamnati, kuma tuni gwamnatin tarayya ta karbi 9 daga cikin jiragen sama 20 na horo da aka tanada domin gudanar da shirin cikin sauki.