Home Labarai Jirgin Qatar ya yi saukar gaggawa don wata mai naƙuda wacce ta haihu kafin ya taɓa ƙasa

Jirgin Qatar ya yi saukar gaggawa don wata mai naƙuda wacce ta haihu kafin ya taɓa ƙasa

0
Jirgin Qatar ya yi saukar gaggawa don wata mai naƙuda wacce ta haihu kafin ya taɓa ƙasa

Kamfanin jiragen sama na Qatar Airways ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama a birnin Karachi na kudancin Pakistan, in ji Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama, CAA, ta Pakistan a yau Talata.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta CAA ta fitar ta ce jirgin ya yi saukar gaggawar ne da yammacin jiya Litinin a filin jirgin sama na Jinnah na Karachi bayan wata mata mai juna biyu, ƴar kasar Philippines ta da naƙuda.

Hukumar ta CAA ta ce an ba matar agajin farko a cikin jirgin, inda ta kara da cewa likita da motar daukar marasa lafiya sun kasance a lokacin da jirgin zai⁴ sauka, yayin da aka haifi yaron a lokacin.

Sanarwar ta ce an kai matar da yaronta zuwa asibitin yankin, kuma jirgin ya tashi cikin sa’o’i biyu da sanyin safiyar Talata.

Jirgin ya taso ne daga Doha zuwa Manila, a cewar CAA.