
Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam, JNI reshen karamar hukumar Zaria ta maka Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli a kotu bisa zarginsa da karkatar da cekin kuɗi na naira miliyan 20 da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba ta.
JNI ta ce an biya cekin cekin ne ga kungiyar a matsayin diyyar karɓe filinta na Kwalejin Larabci ta Jama’atu, ɓangaren maza, domin aikin hanyar jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Zariya a wani ɓangare na aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano.
A karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Afrilu, a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar da sakataren JNI reshen Zazzau, Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ɗin.
Masu shigar da ƙara sun yi ikirarin cewa sarkin ya rusa shuwagabancin JNI ne a matsayin wata hanya ta rufe musu baki.