
Kimanin sa’o’i 48 da barranta kansa da ga yunƙurin da wasu ƙungiyoyi ke yi na shigar da shi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, a ƙarshe dai tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi amai ya lashe, inda ya yanke shawarar tsayawa takarar.
A ranar 9 ga watan Mayu, an jiyo Jonathan ɗin ya ƙi amincewa da fim ɗin takarar shugabancin ƙasa da a ka ce wasu kungiyoyin Fulani da almajirai sun saya masa.
An jiyo Jonathan na cewa cin fuska ne a ce mutane sun saya masa don ba tare da amincewarsa ba, amma sai ga shi ya yi mi’ara-koma-baya.
Wata majiya mai tushe da ga ɓangaren Jonathan da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa lallai tsohon shugaban kasar ya shiga jam’iyyar APC a hukumance, bayan da ya yi rajista a mazaɓarsa ta Otuoke da ke Bayelsa.
Majiyar ta bayyana cewa a na sa ran a yau Alhamis Jonathan zai miƙa fom din takarar ta sa na jam’iyyar APC wanda Fulani da almajirai ɗin su ka saya masa a farkon makon nan.
A cewar majiyar, tsohon shugaban kasar ya samu goyon bayan adadin da ake bukata na wakilan jam’iyyar APC daga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.
“Wasu jiga-jigan jam’iyyar da dama sun yi ta kiran Jonathan suna yi masa mubaya’a da kuma goyon bayansu,” majiyar ta bayyana.
Majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa cewa a yammacin jiya Laraba wasu manyan shugabannin Afirka sun kira Jonathan a ranar Litinin da ta gabata don ba shi shawarar “ya tsaya takara domin amfanin Nijeriya.
Majiyar ta ambato wasu daga cikin shugabannin Afirka na shaida wa Jonathan cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali kuma “tana bukatar shugaba mai hada kan al’umma kamar Jonathan a wannan lokaci”.