
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ƙi amincewa da fom ɗin Naira miliyan 100 na takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC da Fulani makiyaya da almajirai su ka saya masa.
Ikechukwu Eze, mai baiwa Jonathan shawara kan harkokin yaɗa labarai a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, ya ce cin fuska ne ga al’umma su saya masa fom ɗin ba tare da amincewar sa ba.
Sanarwar ta kasance martani ne kan saya wa tsohon shugaban kasar fom domin ya yi takarar shugabancin ƙasa a a zaɓen 2023.
“Mun samu labari cewa wata kungiya ta sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da sunan tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan.
“Muna so mu bayyana a fili cewa Dr Jonathan bai san da wannan tayin ba kuma bai ba da izini ba.
“Muna so mu bayyana cewa idan tsohon shugaban kasar na so ya tsaya takara, zai bayyana aniyarsa ga jama’a kuma ba zai sanar ta bayan gida ba,” in ji Mista Eze.
Sai dai ya nuna jin dadinsa ga gagarumin goyon baya da ƴan Nijeriya su ke nuna wa Jonathan Kano ya fito ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023.
Tun da fari, Shugaban Fulani makiyaya da almajirai, Ibrahim Abdullahi a baya ya shaidawa manema labarai bayan sayan fom ɗin cewa a sake zaɓar Jonathan domin ya kammala aikin da ya fara.