Home Labarai Ni ba juya bace, mai-ɗakin gwamnan Edo ta yi martani ga Adams Oshiomhole

Ni ba juya bace, mai-ɗakin gwamnan Edo ta yi martani ga Adams Oshiomhole

0
Ni ba juya bace, mai-ɗakin gwamnan Edo ta yi martani ga Adams Oshiomhole

Matar Gwamnan jihar Edo, Besty Obaseki ta shawarci matan da basa haihuwa kan kada gwiwarsu tayi sanyi domin zasu iya cika muradunsu ta mabanbanta hanyoyi ba iya zama uwaye ba.

Daily Trust ta rawaito cewa matar Gwamnan na bayani ne a ranar Asabar a wani taron tattaunawa ta kafar Internet wanda matan Edo dake zaune a kasashen ketare suka shirya ga dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar, Asue Ighodalo.

“Ni ba juya bace; ina cikin nishadi kuma ina cimma burina”, inji ta.

Tana mayar da martani ne kan tambayar da wata mata tayi mata game da kalaman tsohon Gwamna, Sanata Adams Oshiomhole kan cewa bata haihuwa.

Oshiomhole, yayi bayanin ne don mayar da martani kan kalaman Besty wacce ta ce, Ighodalo ne kadai yake da mata a wadanda suke neman kujerar Gwamnan jihar.

Ta ce ta taba samun barin ciki wanda dan yazo a mace.