Home Labarai Kabiru Gaya ya lashe zaben fidda gwani na Sanatan Kano ta kudu a APC

Kabiru Gaya ya lashe zaben fidda gwani na Sanatan Kano ta kudu a APC

0
Kabiru Gaya ya lashe zaben fidda gwani na Sanatan Kano ta kudu a APC

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka yi na Sanatan Kano ta kudu da kuri’u sama da Miliyan daya. Yayin da Abokin takararsa Hon. Kawu Sumaila ya zo na biyu da kuri’u dubu dari uku da kadan.

Wannan zabe dai na Sanatan Kano ya kudu na daga cikin zaben da yake mai zafi a jihar Kano, inda aka dinga musayar zafafan kalamai tsakanin ‘Yan takarar biyu.

Tuni Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya karbi sakamakon zaben sannan kuma ya taya Sanata Kabiru Gaya mutane lashe wannan zabe.