Home Nishaɗi Kabiru Nakwango na nan lafiya ƙalau bai mutu ba — El-Mustapha

Kabiru Nakwango na nan lafiya ƙalau bai mutu ba — El-Mustapha

0
Kabiru Nakwango na nan lafiya ƙalau bai mutu ba — El-Mustapha

 

Shahararren jarumin finafinan Kannywood, Abba El-Mustapha, ya ƙaryata labarin cewa fitaccen jarumin masana’antar, Alhaji Kabiru Nakwango ya rasu.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa a yau Litinin ne a ka tashi da jita-jitar cewa Nakwango ya riga mu gidan gaskiya, inda kabarin ya karaɗe kafofin sadarwa.

Sai dai kuma a wani martani na gaggawa, El-Mustapha ya wallafa a shafinsa na facebook, inda ya ce tuni ma su ka yi waya da Nakwango, har ma ya ce masa yana gonarsa yana ta aiki.

“Yanzu mu ka yi waya da Malam Kabiru Nakwango, mu ka gaisa muka ɗan taɓa barkwancinmu da muka saba yi dashi.

” Daga ƙarshe ya ce in gaishe masa da masoyansa na page ɗi na.

“Ya ce shi yanzu haka ma ya tafi gonarsa domin gewaya”. Inji Abba El-Mustapha.