
Fitacciyar ‘yar fafutikar dawo da matan Chibok da aka sace, karkashin kungiyar BringBackOur Gils BBOG, Aisha Yesufu ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kada ya sake neman tsayawa zabe a 2019.
‘Yar fafutikar tace, goyon bayan da zata iya baiwa Shugaban kasa daya ne tak, shi ne ta taimaka masa ya tattara i-nasa i-nasa ya bar fadar gwamnati in wa’adinsa ya kare, inji Aisha Yesufu.
Madam Yesufu ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, inda tace zata taimakawa Shugaban kasa wajen ganin ya isa Daura lafiya a 2019 bayan karewar wa’adin mulkinsa.
Tace “In sha Allah zan taimakawa shugaba Muhammadu Buhari da addur fatan ya kammala lafiya ya koma mahaifarsa Daura a 2019”.
Idan ba’a manta ba, a kwanakin baya Aisha Yesufu tayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus, a cewarta ya gaza matuka. Abin ya tayar da kura akai ta yi mata martanikan wannan kira.
Ita dai Aisha Yesufu da kungiyarta ta BBOG sun sha sukar salon tafiyar da mulkin gwamnatin Buhari da jam’iyyar APC.