Home Labarai Kada wani sarki ya kuma naɗin sarauta ba da izinin mu ba — Gwamnatin Zamfara

Kada wani sarki ya kuma naɗin sarauta ba da izinin mu ba — Gwamnatin Zamfara

0
Kada wani sarki ya kuma naɗin sarauta ba da izinin mu ba — Gwamnatin Zamfara

 

 

 

Gwamnan jihar Zamafara da ke arewa Bello Matawalle, ya hana Sarakunan jihar nadin sarauta har sai sun samu amincewar gwamnatin jihar.

A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yada labari da sadarwa, Zailani Bappa ya fitar, gwamnan ya ce ”Daga yanzu an umarci duk Sarakuna, da Hakimai, da Dagatai da ke jihar da su nemi amincewar gwamnatin jihar kafin su nada kowa, a kowanne mukami na Sarautar gargajiya”.

BBC ta rawaito sanarwar ta ci gaba da cewa ”umarnin ya zama wajibi ne domin kauce wa gurbata tsarin sarautar gargajiya, daga yanzu babu Sarki, ko Hakimi ko Dagacin da zai nada kowanne mukamin Sarauta, ba tare da samun amincewa da sahalewar gwamnatin jiha ba”.

”Bin wannan doka ya zama wajibi, domin kuwa gwamnati ta tanadi kwakkwaran mataki ga duk wanda ya saba wa dokar”, in ji sanarwar.