
Katafaren gidanan nan da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubaka, da matarsa ta hudu Jennifer Douglas suka mallaka a jihar Maryland dake kasar Amurka, an kada masa gwanjo.
Tun a shekarar 2005 ne da hukumar binciken kwakwaf ta kasar Amurka suka gudanar da wani bincike a gidan lokacin da ake zargin wani dan majalisar dokokin Amurka William Jefferson zargin cin hanci da almundahana.
Katafaren gidan mai daki bakwai, gidan mai launin rawaya wanda ke lamba 9731 Ave, Potomac a jihar Maryland. An kiyata kudin gidan da zambar kudi dalar Amurka miliyan 3.25 a watan Janairun da ya gabata. Sai dai kuma an sayar da gidan akan kudi dala miliyan 2.95 a watan Fabrairun da ya gabata bayan an kada masa gwanjon farko.
Wannan su ne hotunan gidan da PREMIUM TIMES suka wallafa
![Atiku's US mansion [Photo Credit: Zillow - www.zillow.com]](https://i2.wp.com/storage.googleapis.com/stateless-dailynigerian-com/2018/03/8abb0721-atiku-mansion-4.jpg?resize=284%2C189&ssl=1)
![Atiku's US mansion [Photo Credit: Zillow - www.zillow.com]](https://i1.wp.com/storage.googleapis.com/stateless-dailynigerian-com/2018/03/d651d418-atiku-mansion-6-300x199.jpg?resize=300%2C199&ssl=1)
![Atiku's US mansion [Photo Credit: Zillow - www.zillow.com]](https://i0.wp.com/storage.googleapis.com/stateless-dailynigerian-com/2018/03/3d5b276f-atiku-mansion-1-300x195.jpg?resize=300%2C195&ssl=1)
![Atiku's US mansion [Photo Credit: Zillow - www.zillow.com]](https://i2.wp.com/storage.googleapis.com/stateless-dailynigerian-com/2018/03/9a925dd0-atiku-mansion-2-300x200.jpg?resize=300%2C200&ssl=1)
![Atiku's US mansion [Photo Credit: Zillow - www.zillow.com]](https://i1.wp.com/storage.googleapis.com/stateless-dailynigerian-com/2018/03/62c19903-atiku-mansion-7-150x131.jpg?resize=362%2C316&ssl=1)