Home Labarai Kafin harin Kuje sai da SSS ta bada rahotanni 44 amma gwamnati tai watsi da su — Wase

Kafin harin Kuje sai da SSS ta bada rahotanni 44 amma gwamnati tai watsi da su — Wase

0
Kafin harin Kuje sai da SSS ta bada rahotanni 44 amma gwamnati tai watsi da su — Wase

 

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa jami’an tsaron ƙasar nan sun yi watsi da kimanin rahotanni 44 da jami’an tsaron farin kaya SSS su ka bayar kafin harin ta’addancin da aka kai a gidan yari na Kuje.

Wase ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar na jiya Talata a yayin da yake bayar da kudiri a kan ‘Bukatar a dakatar da shirin haramta hayar babura a fadin kasar nan, wanda ɗan majalisa Abubakar Yalleman (APC-Jigawa) ya ƙirƙiro da shi.

A tuna cewa Majalisar Ƙoli ta Tsaro, a zaman ta na kwanan nan, ta bada shawarar hana hawa Babur mai ƙafa biyu a faɗin ƙasar nan da nufin magance matsalar tsaro.

Da yake goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ke shirin dauka na hana zirga-zirgar babura na haya a fadin kasar, Wase ya ce ba za ta yiwu a zuba wa gwamnati idanu ta na yin watsi da bayanan sirri na tsaro ba.

Wase ya ce: “Kalli abin da ke faruwa a yau a Abuja. Magana ta gaskiya, na duba rahotannin DSS na ga cewa rahotannin sirri 44 su ka bayar kafin harin Kuje. Ina mai tabbatar muku da haka, 44 na bi rahotannin ɗaya bayan ɗaya. Kuma duk yana da alaƙa da wannan.

“Babu wani guri da za a kai hari ba tsere da mun samu bayanin sirri daga waje ba, kuma wannan wani bangare ne na fitar da bayanai da suka bayar a kan abin da zai faru, abin da ke faruwa da abin da ba zai faru ba. .”

Ya kara da cewa, “A bisa ka’idarmu na taimakawa gwamnati wajen dakile matsalar rashin tsaro a kasarmu, dole ne mu hada kai da gwamnati.”