
Inuwa Yahaya, gwamnan jihar Gombe, ya ce na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) za ta toshe duk wata kafa ta yin maguɗin zaɓe a zaɓen 2023.
Yahaya ya ce kafin ƙirƙirar na’urar ta BVAS, wasu ƴan siyasa sun yi amfani da na’urar yin zaɓe ta Card Reader su ka riƙa yin aringizon ƙuri’u a zaɓukan da su ka gabata.
Da ya ke jawabi a jiya Talata a karamar hukumar Akko ta jihar Gombe, gwamnan ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bisa bullo da na’urar ta BVAS.
Yahaya ya ce yana da yakinin cewa ‘yan takarar jam’iyyar APC a dukkan matakai za su lashe zabe a jihar a 2023.
“A zaɓukan da su ka gabata, sai ka ga wasu mutane za su zauna a daki su rubuta sakamakon zaɓe, suna bayyana ko wane ne ya lashe zabe, amma da zuwan BVAS, ba ma jin tsoro saboda muna da magoya baya,” inji shi.
Yahaya ya yi kira ga masu son kada kuri’a a yankin da su tabbatar sun karbi katin zabe na dindindin (PVCs).