
Rundunar ƴan sanda a jihar Borno, a jiya Alhamis, ta bayyana cewa mutane 14 ne ke fuskantar shari’a a gaban kotu bisa zargin tada tarzoma a yayin gangamin siyasa a jihar.
Da ya ke yi wa manema labarai karin haske a Maiduguri kan nasarorin da rundunar ta samu a cikin shekarar da mu ke bankwana da ita, kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Abdu Umar, ya ce ana tuhumar wasu kararraki bakwai a gaban kotu.
Ya ce ƴan jam’iyyar APC 12 da wasu ƴan jam’iyyar PDP guda biyu ana tuhumar su da laifukan da su ka shafi barazanar tashin hankali da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Sauran tuhume-tuhumen a ke musu sun haɗa da kawo rashin zaman lafiya, tada hankali da kuma haddasa fargaba a cikin al’umma, da sauransu.
CP ɗin ya ce rundunar ta dukufa wajen ganin an gudanar da sahihin zabe kuma bisa ga umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasar na kama wa tare da gurfanar da mutane ko kungiyar da ke tayar da tarzoma.
Umar ya ci gaba da cewa rundunar za ta ci gaba da hada kai da sauran jami’an tsaro domin ganin an samu yin zaben cikin zaman lafiya.