Home Labarai An kai gwamnatin Nijeriya ƙara kotu bisa zargin Buhari da shirin mayar da harkar ƴan sanda ta zama kasuwanci

An kai gwamnatin Nijeriya ƙara kotu bisa zargin Buhari da shirin mayar da harkar ƴan sanda ta zama kasuwanci

0
An kai gwamnatin Nijeriya ƙara kotu bisa zargin Buhari da shirin mayar da harkar ƴan sanda ta zama kasuwanci

 

Cibiyar kare Haƙƙin ɗan Adam da Ci gaban Rayuwa, CEFSAN ta kai gwamnatin Nijeriya ƙara a babbar kotu da ke Abuja a bisa zargin shirin mayar da harkar ƴan sanda ta zama kasuwanci ta hanyar ƙirƙirar wani sabon ɓangare a ciki.

A takardun ƙarar da jaridar DAILY NIGERIAN ta gani, idan sabon ɓangaren ya soma aiki, to ɓangarorin ƴan sanda na musamman irin su mofol da sashin yaƙi da ta’addanci, za su rika baiwa masu kuɗi da manyan mutane da ma ma’aikatu kariya sai a riƙa biyan su.

Hakan ya saɓa da yadda rundunar ƴan sanda ta ƙasa ta saba, inda ɓangare na kariya, SPU, wanda su ne da alhakin irin wannan aikin.

“Wannan sabon tsarin zai baiwa masu kuɗi da manyan ƙasar nan su riƙa samun tsaro na musamman, inda talakawan ƙasa kuma sai a bar su a hannun ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane,” in ji Adam Lawan, ɗaya da ga cikin lauyoyin da su ka shigar da ƙarar a madadin CEFSAN wanda ya shaidawa DAILY NIGERIAN.

“wannan tsarin zai maida harkar ƴan sanda ta zama gurin samun kuɗi inda kawai masu kuɗi za su shiga yanar gizo su ce su na son ɗan sanda yanzu ya je kuma ya kare su su je inda za su je kuma ba kuɗi,” in jinshi.

Ya ƙara da cewa ba abin da tsarin zai kawo sai dai ƙara nuna raunin aikin ɗan sanda a ƙasar, musamman idan a ka yi duba da rashin tsaron da ke damun ƙasar.