
Ƙungiyar matasa mai suna Arewa Decide, Naka Sai Naka, sun ce ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya je yai kwanciyar sa za su kaɗa masa ƙuri’u har ya lashe zaɓe a Kano.
Rabi’u Husseini, Shugaban ƙungiyar na shiyyar Arewa ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a jiya Talata a Kano.
Ya ce sun ƙuduri aniyar zaɓen Atiku ne sabo da ya fi dukkanin ƴan takarar cancanta.
A cewar Husseini, Atiku ya fi duk sauran ƴan takarar shugabancin ƙasa zurfin tunani da hikima wajen kawo wa ƙasa ci gaba.
“Batun da ya yi na buɗe bodojin Nijeriya batu ne mai matukar amfani domin a ko ina a duniya ba a kulle boda.
“Mu mun san Atiku yana kaunar talakawa kuma zai samar da ayyukan yi kamar yadda yanzu ya ke da ma’aikata sama da dubu 300 a kamfanonin sa.
“Mun san shi kadai ke mu ke da yaƙinin zai gyara ƙasar mu Nijeriya. Shi ya sa mu ka je ya kwantar da hankalinsa za mu kawo masa Kano, da ma Arewacin Najeriya baki ɗaya,” in ji Husseini.