Home Labarai An kai masu gadi kotu bisa zargin satar ‘cornflakes’

An kai masu gadi kotu bisa zargin satar ‘cornflakes’

0
An kai masu gadi kotu bisa zargin satar ‘cornflakes’

 

 

An gurfanar da wasu masu gadi su biyu a gaban wata Kotun Majistare a Jihar Legas bisa zargin satar kayan 400 na ‘Cornflakes’ wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 2.1.

Tun da fari, ƴan sanda sun gurfanar da masu gadin, Monday Ulelu da Mubarao Azeez ne bisa zargin had6in baki da kuma yin sata.

Sai dai kuma duk su biyun sun musanya zargin da a ke yi musu a gaban kotu.

Ɗan sanda mai gabatar da kara, Sifeto Benedict Aigbokhan, ya shaida wa kotun cewa masu gadin sun saci katan 400 na ‘Nabeu cornflakes’ wanda kuɗinsu ya kai miliyan N2.1, mallakar wata mai suna Bintu Osifodumn.

Ya ƙara da cewa, waɗanda ake zargin suna aikin gadi ne a gidan da aka adana kayan, a ranar 13 ga Yuni, a yankin Ikotun, a birnin Legas kuma suka kasa ba da kwakkwaran bayani kan yadda aka yi kayan suka bace.

A cewarsa, wannan laifi ne da ya saba wa Sashe na 287 da na 411 na Kundin Dokokin Jihar Legas na 2015.

Daga bisani, alkaliyar koton, K. A. Ariyo ta ba da belin wadanda ake zargin kan N500,000 kowannensu tare da gabatar da shaidu guda biyu-biyu.

Ta kuma sharɗanta cewa tilas shaidun su kasance ma’aikata, su kuma nuna shaidar biyan haraji ga Gwamnatin Jihar Legas.

Daga nan, mai shari’ar ta dage cigaba da sauraren karar zuwa 28 ga Agusta.