
A yau Talata ne aka gurfanar da wani matashi ɗan shekara 23 mai suna Kehinde Ogunniyi a gaban wata kotun Majistare ta Badagry da ke Jihar Legas bisa zargin mallakar makami mai haɗari ba bisa ƙa’ida ba.
Ogunniyi, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ana tuhumarsa da mallakar makami mai haɗari ba bisa ka’ida ba.
Lauyan mai gabatar da kara, Ayodele Adeosun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Yuli, da misalin karfe 2 na dare a kofar CCECC da ke titin Badagry a Legas.
Adeosun, mai muƙamin sifeto, ya ce wanda ake tuhumar, an kama shi ne da wata doguwar wuka a cikin sa’o’in da bai kamata a ga mutum a wannan lokacin ba na dare, kuma ya yi yunkurin aikata laifi da niyyar yi wa masu ababen hawa ƙwace.
Laifin, inji mai gabatar da ƙara, ya saɓawa sashe na 406 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Alkalin kotun, mai shari’a Lazarus Hotepo ya bayar da belinsa a kan kudi naira 50,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Adefioye ya ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Agusta.