Home Labarai Za mu kai NMDPRA kotu bisa iƙirarin ta ba mu N74b bayan ba ta ba mu ba — IPMAN

Za mu kai NMDPRA kotu bisa iƙirarin ta ba mu N74b bayan ba ta ba mu ba — IPMAN

0
Za mu kai NMDPRA kotu bisa iƙirarin ta ba mu N74b bayan ba ta ba mu ba — IPMAN

 

 

 

 

 

 

Ƙungiyar Dillalan Man fetur Mai zaman kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta yi barazanar kai hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya, NMDPRA kotu, kan abin da ta bayyana a matsayin ‘ƙarya’ na cewa ta biya naira biliyan 74 kudin dakon mai ga ƴan kasuwar.

Hukumar NMDPRA, a ranar Laraba ta ce ta biya ƴan kasuwa Naira biliyan 74 a cikin watanni bakwai da suka gabata.

Da ta ke mayar da martani ga wannan iƙirarin, IPMAN, ta bakin Shugabanta, reshen Arewa, Bashir Danmalam, ta ce iƙirarin ba gaskiya ba ne, domin ba a biya ‘ya’yans ƙungiyar ba, inda ya ƙara da cewa “sai dai idan an biya ƴan kasuwar aljanu a ka biya.”

A wata zantawa da manema labarai a Kano a jiya Alhamis, Danmallam
ya ƙalubalanci hukumar NMDPRA da su fito da sunayen duk ƴan kasuwar da aka biya domin tabbatar da ikirarin na su.

Da ga nan ne sai Danmallam ya yi barazanar gurfanar da hukumar a gaban kuliya saboda ta sanar da biyan kuɗaɗen dako ga mambobi IPMAN bayan da kuma ba ta bada kuɗin ba.

“Na yi mamakin iƙirarin biyan Naira biliyan 74 da Shugaban Hukumar, Faruk Ahmed Maishanu ya yi, ko dai an gaya masa ƙarya, ko kuma bai san abin da ke faruwa a wurin ba.

“Wa da wa aka baiwa kudin? Na san wasu ƴan kasuwa da ake bin kowannensu ke bin bashin Naira biliyan 10. Don haka a ce hukumar ta biya Naira biliyan 74 ga ‘yan kasuwar ba gaskiya ba ne.

“Don haka, za mu iya yarda da biyan kuɗin da aka ce kawai idan an biya kuɗin ga “‘yan kasuwa na boge”.

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta sallami wannan mutumin saboda bai cancanta ya riƙe irin wannan muƙamin ba ganin cewa bai san abin da ke faruwa a can ba.

Ya yi nuni da cewa gazawar hukumar wajen sasanta ikirari na jigilar ‘yan kasuwar da ya kai kimanin Naira biliyan 500 ne ya janyo karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan.

Danmalam ya ce bisa binciken da kungiyar IPMAN ta gudanar, an gano cewa a baya-bayan nan ne Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya saki sama da Naira biliyan 70 ga hukumar domin biyan ‘yan kasuwa da har yanzu ba a biya su ba.

Ya koka da cewa kafin yanzu ana biyan mambobinsu kuɗaɗensu a cikin wata ɗaya ko biyu saɓanin yadda ake biyansu a halin yanzu.