
Yadda aka akaiwa jirgin kasa dake safara daga Abuja zuwa Kaduna hari. Abin ya faru ne kamar almara a yayin da jirgin kasa ya taso daga Abuuja zuwa Kaduna wasu mahara a tashar jirgin dake Rijana suka bude masa wuta.
Jirgin ya dauko daruruwan fasinja daga Abuja zuwa tasharsa dake Rigasa, a ranar Talata aka kaiwa jirgin hari akan hanyarsa ta zuwa Rigasa jihar Kaduna a daidai Rijana.
Babu wanda ya samu rauni a cikin fasinjojin dake cikin jirgin.
Daya daga cikin wadan da suka hau jirgin zuwa kaduna, Olushegun Giwa, ya bayyana yadda abin ya faru da misalin karfe 7:00 na yamma a daidai tasahar jirgin dake Rijana, kilomita 70 kafin a isa tashar Rigasa dake Kaduna.
“Jirginu ya taso daga babbar tasharsa ta Idu dake Abuja, ya taso dag Abuja zai nufi tashar Rigasa dake kaduna”
“Mun ji harbin kan mai uwa da wabi a jikin jirginmu daidai lokacin da muka iso tashar Rijana a kauyen na Rijana. Mun godewa Allah tagar jirgin irin wadda harsashi baya hudawa ce, wannan shi ne yasa harsashin bai iya hudawa ya shigo cikin jirgin ba”
“Dukkan fasinjojin dake cikin jirgin sun rude da kuwwa suna cewa mun godewa Allah, a lokacin da suka iso tashar jirrgin dake Rigasa, mutane sai murna suke da suka ga sun iso lafiya”
A cewar fasinjan.
Daman can a baya, kauyikan Rijana da Katari da kuma Jere sun zama gurare mafiya hadari a hanyar Kaduna zuwa Abuja tun kusan shekaru biyu da suka wuce.
A cewar wani rahoto, da yawan manyan ‘yan siyasa da suka kunshi Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya sukan hau jirgin kasan ne daga Abuja zuwa Kaduna”
Haka kuma, sabida dalilai na tsaro ya sanya ‘yan majalisun suka gwammace hawa jirgin da su hau manya manyan motocinsu na alfarma.
Wani bincike ya tabbatar da cewar, masu manyan motoci na alfarma sun tsoron bin hanyar kaduna zuwa Abuja, domin masu yin garkuwa da mutane cikin sauki suke kamasu su yi garkuwa da su, a sabida haka ne, suka gwammace su hau jirgin kasan ya kaisu Kaduna daga Abuja sabida dalilai na tsaro.