Home Kanun Labarai Kalaman Buhari sun nuna jahilcinsa kan harkar Gwamnati – Obasanjo

Kalaman Buhari sun nuna jahilcinsa kan harkar Gwamnati – Obasanjo

0
Kalaman Buhari sun nuna jahilcinsa kan harkar Gwamnati – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya mayar da martani kan zargin da Shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari yayi masa na yin badakalar biliyoyin dalolin kan harkar samarda wutar lantarki, inda Buhari ya bayyana cewar babu wutar kuma babu kudin, ga tarin bashi na fitar hankali.

Sai dai obasanjo ya magantu kan wannan zargi, inda ya fitar da wata sanarwa ta hannun kakakinsa Kahinde Akinyemi a birnin Abekuta na jihar Ogun. Obasanjo ya bayyana cewar shi a shirye yake a kafa kwamatin bincike akansa domin kar a bata masa suna kan wannan batu da ake ta yamadidi da shi.

Obasanjo ya bayyana cewar sam SHugaba Buhari ya jahilci harkar Gwamnati matukar yayi masa wannan zargi haka ba tare da wasu kwararan shaidu ko dalilai ba. Gaskiya akwai abin mamaki idan har Shugaba Buhari ya fahimci ma abinda yake magana akansa, yace domin abubuwa suna nan a rubuce.

“Domin kiyayewa, Obasanjo ya sha yin bayani kan wannan batun kudaden wutar lantarki, yace ko a cikin littafinsa da yawallafa mai suna “My Watch” ya yi bayani dalla dalla akan wannan batun kudaden wutar lantarkin da ake zargin yayi sama da fadi da wadannan biliyoyin dalolin”

“Muna fatan Shugaban kasa da ‘yan kanzaginsa zasu kaaranta babi na 41 da 42 da 43 har zuwa na 47 a cikin wannan littafi da Obasanjon ya wallafa, domin karanta dukkan bayanan da suka shafi batun kudaden samar da wutar lantarki da ake zarginsa akan su”