
Wani matashi dan shekara 21 mai suna Micheal Arigbabuwo ya mutu a wani bikin zagayowar ranar haihuwarsa bayan da ake zargin ya yi haɗin kauri na ƙwayoyi masu karfin gaske domin ya ji garau.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan a sahihin shafinsa na Twitter da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya gani a yau Lahadi.
Hundeyin, Sufeto na ƴan sanda, ya ce lamarin ya faru ne a jiya Juma’a a unguwar Ikorodu da ke Legas, inda ya jaddada cewa an kama abokansa uku da ke wajen liyafar.
Kakakin ya ce bayanan da ƴan sanda suka samu a Ikorodu sun nuna cewa da misalin karfe 7:30 na yamma, a ranar Juma’ar ne aka samu wani kira na gaggawa cewa wasu ’yan kungiyar Yahoo Yahoo sun kawo gawa zuwa yankin Igbogbo da ke Ikorodu.
“tuni a ka tashi jami’an binciken ƙwaƙwaf su ka ziyarci inda lamarin ya faru kuma suka dauki hotunan wajen. An kama wasu matasa uku masu shekaru tsakanin 23 da 24.
“Wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa marigayin ya sha hayaki ne sosai ya kuma ɗirki maganin codeine a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar ɗaya daga cikin abokansu da aka gudanar a yankin Igbogbo a Ikorodu.
“Wadanda ake zargin sun kara da cewa daga bisani sai marigayin ya fara haki. Nan da nan a ka garzaya da shi asibiti, inda ya ce ga garinku nan,” inji shi.
PPRO ɗin ya ce an ɗauke gawar an ajiye ta a babban asibitin Ikorodu domin gudanar da bincike.
Mista Hundeyin ya gargadi matasa kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa, miyagun kwayoyi za su kawo karshen rayuwarsu cikin bala’i.
“Tunanin shan kwayoyi? Ku sake tunani domin babu wani abu mai amfani da ke fitowa daga gare ta.
“An fara bincike kan lamarin,” in ji shi.