
Rundunar ƴansandan Nijeriya ta tabbatar da cewa ta kama wasu jami’anta da ke bai wa shahararren mawakin siyasa na APC ɗin nan, Dauda Kahutu Rarara kariya.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga ƴansandan su na bin Rarara a baya har ya shiga mota, inda da ga bisani su ka soma harba bindiga a sama.
Sai dai a wani sako da mai magana da yawun rundunar ƴansanda ta ƙasa, Muyiwa Adejobi ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce rundunar ta yi tir da “rashin kwarewa da kuma halaye na rashin ɗa’a da ƴansandan su ka nuna, inda su ke harba bindiga domin kuranta mawakin na Kano.
“An gano ƴansandan kuma an kama su. Za a kai su hedikwatar ƴansanda domin yi musu tambayoyi da kuma daukar matakan da suka dace,” kamar yadda ya kara da cewa.
Haka kuma ya ce irin wannan ɗabi’a ba ta ƴansanda ba ce kuma ba za su lamunci hakan ba.
Sai dai a wani bidiyon wata hira da aka yi da mawakin, ya musanta cewa ‘yan sandan sun yi harbi domin nishadi inda ya ce wasu ne suka yi niyyar tayar da tarzoma suka yi harbin.
“Mun je muna rabon abinci a Kahutu, sai wasu bata-gari suka shigo suna neman su tayar da tarzoma, a nan wurin ne muka samu matsala ‘yan sandanmu suka yi harbi sama,” in ji Rarara