Home Ƙasashen waje An kama hodar-iblis ta kimanin dala miliyan 8.7 a motar Magajin Gari a Nijar

An kama hodar-iblis ta kimanin dala miliyan 8.7 a motar Magajin Gari a Nijar

0
An kama hodar-iblis ta kimanin dala miliyan 8.7 a motar Magajin Gari a Nijar

 

Rundunar ‘yan sandan Jamhuriyar Nijar ta kama hodar-iblis, wacce a turance a ke kira ‘cocaine’, mai nauyin fiye da kilogiram 200.

An ƙiyasta kuɗin wannan hoda ya kusa dala miliyan 8.7.

Rahotanni sun baiyana cewa an kama hodar ne a cikin motar wani magajin gari, a cewar wasu majiyoyin ‘yan sanda.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda ya rawaito wannan labari ranar Litinin, ya ƙara da cewa an kama magajin garin da direbansa, waɗanda suke cikin motar, da ƙulli 199 na hodar a wani wajen binciken ababen hawa da ke wajen birnin Agadez a ranar Lahadi.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin da ke yaki da miyagun kwayoyi na kasar ya tabbatar da kama fiye da kilogiram 200 na cocaine a Agadez, kodayake bai yi karin bayani ba.

Wasu ƙasashen Yammacin Afirka sun kasance hanyar da ake bi wajen safarar miyagun kwayoyi daga Kudancin Amurka zuwa Turai, kuma a ‘yan shekarun nan an samu karuwar kama miyagun kwayoyi a yankin.