Home Labarai An kama matasan da su kai yunƙurin sace adaidaita-sahu bayan sun baiwa direban alewa mai bugarwa

An kama matasan da su kai yunƙurin sace adaidaita-sahu bayan sun baiwa direban alewa mai bugarwa

0
An kama matasan da su kai yunƙurin sace adaidaita-sahu bayan sun baiwa direban alewa mai bugarwa

 

Wani direban adaidaita-sahu ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu matasa da ya ɗauka su ka bashi alewa mai bugarwa, su ka kuma yi yunƙurin guduwa da machine ɗin nasa a Jihar Kano.

Tun da fari dai, direban ya ce ya dauko fasinjojin ne da ga unguwar ‘bypass’ zai kai su unguwar Tudun Murtala, gidan Atiku Abubakar.

A kan hanyar su ta zuwa inda su ka ce ya kai su, sai su ka yi masa tayin alewa, shi kuwa garin kwaɗayi, ya sa hannu ya karɓe ya kuma jefa ta a baki.

Ya na cikin tsotsar alewa, sai kuwa ta fara yi masa aiki, inda kan ka ce kwabo, ta bugar da shi bai san inda kan sa ya ke ba.

Da ga nan ne sai matasan, Arabiyu Sani da Aminu Mohammed, su ka kai shi gindin wata bishiya su ka kwantar da shi, inda mutanen da ke kusa su ka an kara su ka kuma yi musu tara-tara su ka kame su.

Da ga nan ne a ka miƙa wa ƴan sanda, su kuma su ka kai su kotu, bayan da shi kuma gogan naka mai babur ya riƙa sharar bacci har tsawon kwanaki biyu.

A zaman kotun na jiya Litinin, a Kotun Shari’ar Muslunci da ke zaman ta a Gama PRP, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Isa Rabi’u Kademi, an gurfanar da matasan su biyu, inda a ke tuhumar su da laifuka biyar.

Laifukan sun haɗa da zargin haɗin baki, sata, da yunƙurin kisan kai, kamar yadda Jami’in farin kaya, Detective Aliyu Zainul-Abidin ya fassara ya kuma karanto musu amma su ka musanta.

Da ga nan ne sai kotu ta waiwayi mai gabatar da ƙara, sai ya ce a basu rana za su zo da shaidu.

Alkalin ya sanya 21 ga watan Maris domin cigaba da shari’ar.