Home Labarai An kama matashin da yai basaja ya sace wayar masu jinya a asibitin ƙashi na Kano

An kama matashin da yai basaja ya sace wayar masu jinya a asibitin ƙashi na Kano

0
An kama matashin da yai basaja ya sace wayar masu jinya a asibitin ƙashi na Kano

 

Dubun wani matashi mai suna Abdul’aziz ta cika, bayan da ya ɗaura bandeji a ƙafarsa kamar ya ji rauni, ya shiga cikin marasa lafiya ya sace musu waya.

Lamarin ya faru ne a Babban Asibitin Ƙashi na Dala, a Jihar Kano, a jiya Juma’a, bayan da jami’an tsaron asibitin su ka cafke shi ya ɗauke wa wani majiyyaci wayar salula.

Ismail Ismail, ɗaya da ga cikin jami’an tsaron asibitin, ya ce ya ga matashin yana ta zirga-zirga ne sai jikin shi ya bashi cewa matashin bashi da gaskiya.

“Da na ga yana ta zirga-zirga, sai ban ce masa komai ba, sai na sa masa ido ina ganin motsinsa. Na san dai a asibitin nan, marasa lafiya ba sa zirga-zirga irin haka.

“Sau uku yana wuce wa ta inda na ke duty, can sai na ga ya shiga wani ɗaki. Bai dade da shiga ba, sai na ji an saka ihun ɓarawo, sai kuwa na gan shi ya fito a guje. Sai na bishi da ni da sauran abokan aiki na.

“Mu na zuwa wani lungu da ya shige, sai muka tarar har ya cire rigarsa, shine mu ma damƙe shi,” in ji Ismail.

A cewar Abdul’aziz, ya yi basaja ne domin ya samu kuɗin motar komawa garin su.

Ya ce shi wannan bandejin ba na ƙarya ba ne sabo da dama a kwai rauni a ƙafarsa, shine ya ɗaura shi.

Bayan ya amsa laifinsa, Abdul’aziz ya roki a yi masa afuwa.

Jami’an tsaron asibitin sun ce za su miƙa shi ga ƴan sanda da zarar sun kammala bincike.