
Kotu ta sake kama ɗan bayan Manchester City, Benjamin Mendy da ƙarin wani laifin na fyaɗe.
A ranar 26 ga watan Agusta ne dai a ka fara kai Mendy, ɗan ƙasar Mai shekara 27 kotu, inda a ke tuhumar sa da laifukan fyaɗe har guda 7 da kuma na cin zarafi guda 1 a kan ƴan mata 5.
Tun da fari, kafin a kai Mendy kotu, an yi masa ɗaurin talala, amma bayan an kai shi kotun Chester Crown, sai a ka ɗage ɗaurin, amma kuma da ga baya sai kotun ta dawo da ɗaurin na talala.
A na zargin laifukan da a ke canjin Mendy da su ya aikata su ne a tsakanin watan Oktoba 2020 da kuma Agusta 2021.
Tun farkon watan Oktoban 2021 a ka hana shi beli kuma har yanzu ɗan wasan na zaune a gidan yari.
Tun farkon Shari’ar ta sa ne kungiyar ta sa, Man City ta dakatar da shi.