Home Labarai An kama mutane 4 kan zargin kashe dalibar jami’a a Kogi

An kama mutane 4 kan zargin kashe dalibar jami’a a Kogi

0
An kama mutane 4 kan zargin kashe dalibar jami’a a Kogi

Yansanda sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a kisan wata dalibar jami’ar tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi.

Ana zargin wani matashi da sace dalibar mai shekaru 17 da ke aji na farko a jami’ar, inda kuma ya kashe ta.

Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar, SP Williams Ovye-Aya, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai.

Onye-Aya ya ce babban wanda ake zargin ya hada kai da abokanan sa uku wajen aikata laifin.

“Jami’an ‘yan sandan Nijeriya dake sashin binciken manyan laifuka a jihar Kogi, sun kama Jeremiah Paul-Awe na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar 11 ga watan Satumba.

” Paul shi ne ya sace dalibar kuma ya kashe ta.

“Mun karbi korafi daga Stephen Oluwoyo cewa ‘yar sa ta bata kuma baya samun ta.

” Mahaifin nata ya kara da cewa ya samu sakon waya daga wata sabuwar lamba cewa an yi garkuwa da ‘yar sa kuma ana neman kudin fansa”, inji shi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wadanda ake zargin sun amsa laifin su.

Sannan za a gurfanar dasu gaban kotu da zarar an kammala bincike.