
Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun kama mutane 18 da ake zargi da hannu wajen kitsa rikicin addini a jihar Kaduna ranar Litinin a kasuwar Magani dake yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
An bayyana hakan ne jim kadan bayan da dukkan sassan jami’an tsaro na jihar Kaduna suka ziyarci yankin da abin ya faru a kasuwar magani domin ganin irin dumbin barnar da rikicin ya haifar.
Tawagar wadda Shugaban Kwamnadan rundunar soji ta daya dake jihar Kaduna Manji Janar Mohammed Mohammed ya jagoranta, ta kunshi kwamishinan ‘yan sandan jihar Austin Iwar da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya Mohammed Wakil.
Sauran ‘yan tawagar su ne, Shugaban hukumar tsaro ta NSCDC AM Bunu damai baiwa Gwamnan jihar Kaduna shawara ta fuskar tsaro Kanar Yakubu Yusuf da kuma mai taimakawa Gwamnan Kaduna ta fuskar hulda da kafafen yada labarai Samuel Aruwan.
A jawabinsa yayin da suka ziyarci garin, Kwamandar rundunar soji ta Kaduna ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya a yankin da su yi kira ga jama’arsu su zauna da juna lafiya.
Mista Mohammed ya roki al’ummar da su yi hakuri su zauna da juna lafiya su manta da duk wasu bambance bambance dake tsakaninsu, kuma su daina halaka dukiyoyin juna sabida sabanin ra’ayi.
ya kuma tabbatarwa da al’ummar yankin cewar jami’an tsaro suna nan zasu yi aiki babu dare babu rana wajen ganin an dawo da doka da oda a yankin.
A nasa jawabin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Mista Austin Iwar, a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya tabbatar da kama mutane 18 da ake zargi da hannu wajen tayar da wannan rikici.
“Yanzu haka wadannan mutane suna hannunmu, kuma muna nan ana gudanar da bincike” A cewar kwamishinan.
A nasa banganren, Samuel Aruwan, ya bayyana cewar Gwamnatin jihar Kaduna ta yi maraba da labarin kame mutane 18 da rundunar ‘yan sandan jihar ta yi, yace zasu tabbatar an gurfanar da wanda suke da laifi gaban kotu.
Mista Aruwan ya bukaci al’ummar yankin da su yi hakuri su zauna da juna lafiya ba tare da tashin hankali ba.