
Dawowar sa kenan da ga Brazil, sai jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA su ka kama wani Igwedum Uche Benson a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Jihar Legas ɗauke da ƙullin hodar iblis da ya ɓoye a al’aurarsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta ce an kama Igwedum a filin jirgin sama na Legas a ranar Litinin 20 ga watan Yuni, lokacin da ya sauka daga jirgin Ethiopian Airlines daga Sao Paulo, Brazil daga Addis Ababa.
Sanarwar ta ce, binciken farko da aka gudanar ya nuna wanda ake zargin ya haɗiye ƙulli 50 na hodar iblis kafin ya tashi daga ƙasar Brazil, sannan ya kasayar da ƙulli 48 a Addis Ababa inda ya mika su ga wani mutum.
Sai dai ya yi ikirarin cewa bai iya fitar da sauran ƙulli biyu da suka rage ba, a lokacin da ya ke dakin otal da ke Addis Ababa ba kafin ya hau jirginsa, amma daga baya ya fitar da su a cikin banɗakin jirgin a lokacin da ya tashi daga Habasha zuwa Legas.