Home Siyasa An kama shugabannin PDP bisa farfasa kaya da wargatsa taron ɗaya ɓangaren jam’iyar a Kano

An kama shugabannin PDP bisa farfasa kaya da wargatsa taron ɗaya ɓangaren jam’iyar a Kano

0
An kama shugabannin PDP bisa farfasa kaya da wargatsa taron ɗaya ɓangaren jam’iyar a Kano

 

Ƴan Sanda a Jihar Kano sun cafke wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP, tsagin Shehu Wada Sagagi, bisa farafsa kaya da wargatsa ganawar da shugabannin jam’iyar, tsagin Aminu Wali ke yi a otal ɗin Tahir Guest Palace.

Waɗanda a ka kama sun haɗa da Ma’ajin jam’iyya, Idi Zare Rogo; Sakataren kuɗi, Dahiru Arrow Dakata; Shugaban matasa na jiha, Hafizu Bunkure, da kuma shugaban jam’iyar na Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Idi Mariri.

Duk da cewa ƴan sanda ba su ce komai a kan batun ba, wasu majiyoyin tsaron sun baiyana cewa yanzu haka shugabannin jam’iyar na can shelkwatar ƴan sanda ta Kano su na amsa tambayoyi a kan lamarin.

Jaridar Daily Nigerian ta jiyo cewa shugabannin jam’iyar sun shiga dakin da ɓangaren Wali ɗin ke ganawa, inda su ka saka musu duka kan mai-uwa-da-wabi, su ka farfasa na’ura mai ƙwaƙwalwa da sauran kayayyaki, sanan su ka yi awon-gaba da takardu muhimmai da wasu na’urar mai ƙwaƙwalwa.

Wasu majiyoyi sun ce ɓangaren Sagagi, wanda shi kotu ta tabbatar, na rigima ne da uwar jam’iya ta ƙasa, inda su ke zargin kwamitin zaɓen wakilai na jam’iyar ya ƙulla alaƙa da tsagin Wali.

Shine, a cewar majiyoyin, su ka kutsa kai cikin dakin da ɓangaren Wali ke ganawa, suna zaton cewa su na ɗaukar sunayen wakilan ne tun gabanin yin zaɓen fidda wakilan.