Home Labarai An kama sojoji 2 da laifin kashe Sheikh Aisami, tare da sace motarsa a Yobe

An kama sojoji 2 da laifin kashe Sheikh Aisami, tare da sace motarsa a Yobe

0
An kama sojoji 2 da laifin kashe Sheikh Aisami, tare da sace motarsa a Yobe

 

 

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta kama wasu sojoji biyu da ake zargi da kashe wani shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami da aka hallaka shi a ranar Juma’a, da misalin karfe 9 na dare a kan hanyarsa ta zuwa Gashua daga Kano.

Wasu majiyoyi da dama na cikin gida sun yi zargin cewa sojoji sun kashe malamin ne bayan da ya rage musu hanya daga shingayen binciken sojoji na Nguru zuwa Jaji-maji, wani ƙauye da ke kusa da Ƙaramar Hukumar Karasuwa a jihar Yobe.

Majiyar ta ce sojojin sun harbe shi sannan su ka tsere da motar sa, kirar Honda Accord, kafin daga bisani ƴan sanda su kama su.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya ce sojojin biyu da aka kama su ne Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon na bataliya ta 241 da ke Nguru, jihar Yobe.

Ya ce an kai mutanen biyu zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Damaturu domin gudanar da bincike.

An yi jana’izar fitaccen malamin ne a ranar Asabar a garin Gashua da ke Jihar Yobe, yayin da dubban al’umma, da su ka haɗa ɗalibansa da ƴan uwa da abokan arziki suka yi ta kuka.