
Wani dan najeriya mai kimanin Shekaru 27 da ake kyautata zaton cewa dan kungiyar Boko Haram ne, waddasuke kai hare hare tare da halaka al’umma babu ji babu gani a Najeriya, a cewar mai gabatar da kara na Gwamnati Jamus da ya bayyana hakan ranar Juma’a.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaio cewar, mutumin da aka bayyana sunansa da Amaechi Fred, an kama shine ranar Laraba a Baberiya, bayan da hukumomi a kasar suka sanya sunansa a daya daga cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo.
“An jima ana zarginsa da aikata ayyukan ta”addanci, kasancewarsa mamba a kungiyar ‘yan ta’addar nanta Boko Haram” A cewar sanarwar.
Shi dai Amaechi Fred O. ana kyautata zaton ya shiga kuungiyar Boko haram ne a shekarar2013, kuma ya taimaka matuka wajen kai wasu hare hare a Najeriya.
A yanzu dai ana zarginsa da kashe jama’a da yawa, a wasu manyan hare hare guda biyu, na farko a wata makaranta na biyu kuma a wani kauye, inda ‘yan kungiyar suka sace wasu mata kuma suka bankawa coci coci wuta.
KungiyarBoko Haram dai na kai hare hare tun kusan shekarar 2009, a yunkurinsu na kafa daular Musulunci a Najeriya, haka kuma, kunyiyar ta kai wasu hare haren har da na akunar bakin wake har a kasashen Nijar da Chadi da kuma Kamaru. Fiye da mutum 15,000 ne ake sa ran ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe.
Reuters