Home Labarai An kama wani mutum da bam a banki a Plateau

An kama wani mutum da bam a banki a Plateau

0
An kama wani mutum da bam a banki a Plateau

An kama wani mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba da bam a jikin sa ya shiga harabar wani banki da ke garin Dadin Kowa a yankin Jos ta Kudu a jihar Plateau.

PUNCH Online ta tattaro cewa nan take aka gano bam a jikin mutumin, inda cikin gaggawa aka fallasa shi kuma nan take jami’an tsaro suka rike shi domin kaucewa afkuwar wani bala’i.

Kamar yadda wani mai sharhi kan harkokin tsaro Zagazola Makama ya fitar a yau Talata a shafin sa na X, ya ce jami’an tsaron bankin me su ka yi tamaza su ka dakile harin lokacin da suka hango wanda ake zargin.

Wasu fusatattun mutane sun zo kan wanda ake zargin, inda su ka nemi da a kashe shi.

Daga baya an mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Hoton da ke makale a shafin Makama ya nuna mutumin da bam din a ɗaure a jikin sa.

Sai dai babu tabbas ko wanda ake zargin yana da alaka da wata kungiyar ta’addanci a kasar.